17 Mayu 2015 - 19:05
An Bude Taro a Saudiyyar don Warware rekicin Yemen, 'Yan Ansarullah sun ki halarta

An bude taron kasashen larabawa yau lahadi a birnin Riyadh na Saudiyya da niyyar duba a’lamarin yakin kasar Yemen.

Sai dai kuma bangaren Ansarullah na Houthi,  Yemen dake rike da mafi yawancin kasar   sunki halartan wannan taro.

Taron na zuwa ne yau lahadi, rana ta karshe cikin kwanaki biyar na tsagaita wuta domin kai kayan agaji ga mabukata dake Yemen.

Tsohon Shugaban Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi dake gudun hijira zai yi jawabi a taron na yau.

Bayanai na nuna duk da tsagaita wuta da akayi anyi ta samun hare-hare a wasu sassan kasar ta Yemen.ABNA